Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hai Yan da labarinta na kawar da talauci
2020-07-28 14:24:35        cri
Bayan ta kaura daga yankin tudun Xihaigu na jihar Ningxia zuwa kauyen Yuanlong na garin Minning dake gundumar Yongning na birnin Yinchuan na jihar, Hai Yan ta sami aikin yi, a bana kuma, ta shiga tawagar sayar da kayayyaki ta yanar gizo domin taimakawa masu fama da talauci, inda ta zama wakiliyar sayar da kayayyaki ta yanar gizo, lamarin da ya sa, ta yi nasarar fita daga kangin talauci, lamarin da ya share mata hanyar zama mai matsakaicin wadata.

Tun daga shekarar 2012, jihar Ningxia ta kabilar Hui mai cin gashin kanta ta shafe shekaru 5 wajen sake tsugunar da manoman gundumar Longde ta yankin Yuanzhou dake birnin Guyuan bisa matakai takwas, wadanda a baya suke zaune a yankin hamada zuwa garin Minning, wuri mai ni'ima. Hai Yan ta kaura zuwa garin Minning a wannan lokaci, sa'an nan, ta fara aikin raba kayayyaki a wani kamfanin taimakawa masu fama da talauci, tare da sauran matan garin sama da 90%, sun kuma yi nasarar samun aikin yi a wurin kusa da gidajensu, bisa shirin da aka tsara mai taken "kamfani da sashen taimakawa masu fama da talauci da matalauta".

Sabo da yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, sashen taimakawa masu fama da talauci ya fito da sabon shirin sayar da kayayyaki, inda ya kafa tawagar wakilan sayar da kayayyaki ta yanar gizo. Sa'an nan, Hai Yan da 'yar uwanta sun fara sayar da kayayyaki ta yanar gizo.

Daga mai fama da talauci dake zaune a yankin tudu zuwa wakiliyar sayar da kayayyaki ta kafar bidiyo, a halin yanzu, Hai Yan tana kokarin cimma burinta na zama mai matsakaicin wadata. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China