Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Matakin rashin aikin yi a Afrika ta kudu bai sauya ba a rubu'i na 4 na 2019
2020-02-12 11:17:55        cri

Kididdigar da kasar Afrika ta kudu ta fitar, ta nuna cewa, matakin rashin aikin yi a kasar bai sauya ba, inda ya tsaya kan kaso 29.1 a rubu'i na 4 na shekarar 2019.

Masana tattalin arziki sun sa ran ganin sauyi a kididdigar ta rubu'i na 4, saboda ingantuwar da aka samu wajen samar da ayyukan wucin gadi a lokutan bukuwan karshen shekara.

Da ma an sa ran ci gaban tattalin arzikin kasar a rubu'in na karshe zai tsaya kan kasa da kaso 1.

Da take tsokaci kan kididdigar, jam'iyyar adawa ta Democratic Alliance, ta ce dole ne Shugaba Cyril Ramaphosa ya gaggauta sanar da bullo da shirin da zai rage yawan rashin aikin yi a kasar, yayin jawabin da zai gabatar ga kasar a gobe Alhamis.

Shugaba Ramaphosa ya riga ya bayyan cewa, magance rashin aikin yi da horar da matasa fasahohi na daya daga cikin abubuwan da gwamnatinsa ta ba muhimmanci.

La'akari da rashin tsayayyen lantarki da ake sa ran zai kai watanni 18 masu zuwa, har yanzu ba a kai ga gano irin tasirin da zai yi ga tattalin arziki da kanana sana'o'i a kasar ba. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China