Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta kafa kungiyoyin manoma a galibin kauyuka masu fama da talauci
2020-07-28 10:14:00        cri

Sama da kaso 90 na kauyuka masu fama da talauci a kasar Sin, sun kafa kungiyoyin gama kan manoma, wadanda suka taka muhimmiyar rawa ga kokarin kasar na yaki da talauci.

A cewar wani taro da aka yi kan yaki da talauci ta hanyar masana'antu da ya gudana jiya a birnin Longnan dake lardin Gansu na arewa maso yammacin kasar Sin, an kafa jimilar irin wadannan kungiyoyi 682,000 a yankuna 832 masu fama da talauci, wadanda suka taimakawa mutane kusan miliyan 22 fita daga kangin fatara.

Adadin mutanen karkara dake fama da talauci a kasar Sin, ya sauka daga miliyan 98.99 a karshen shekarar 2012, zuwa miliyan 5.51 a karshen shekarar 2019.

Daraktan ofishin dake jagorantar ayyukan yaki da talauci da raya kasa na majalisar gudanarwar kasar Sin, Liu Yongfu, ya ce yaki da talauci ta hanyar masana'antu ya taka muhimmiyar rawa.

Bisa kiddidigar da ofishin Liu ya fitar, kaso 92 na matalautan kasar sun shiga shirin na yaki da talauci ta hanyar masana'antu. Kuma daga cikin wadanda suka yi adabo da talauci, kaso 72 sun samu tallafi daga shirin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China