Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ainihin adadin masu cutar COVID-19 a Amurka ka iya rubanyawa har sau 6 zuwa 24 a kan wanda aka bayar da rahoto
2020-07-22 13:00:42        cri

Wani sabon rahoto da cibiyoyin kandagarki da dakile yaduwar cututtuka na Amurka suka fitar, ya ce ainihin adadin wadanda ke kamuwa da cutar COVID-19 a kasar, ka iya ninkawa sau 6 zuwa 24, fiye da adadin da ake bayar da rahoto.

Bisa wani nazari kan samfuran gwaji 16,025, cibiyoyin sun yi kiyasin adadin mutanen da garkuwar jikinsu ya nuna sun kamu da COVID-19, ya kai daga kaso 1 a yankin San Francisco zuwa kaso 6.9 a birnin New York.

Nazarin ya gudanar da gwajin garkuwar jiki kan samfuran jinin mutane masu shekaru daban-daban. An tattara samfuran ne daga mutanen da suka je gwajin lafiya tsakanin ranar 23 ga watan Maris zuwa 12 ga watan Mayu, a wasu dakunan gwaji 2.

Sakamakon nazarin wanda aka wallafa a mujjalar lafiya ta JAMA, ya nuna cewa, a kowanne yanki, adadin masu cutar ya zarce adadin da aka bayar da rahoto a lokacin da nazarin ke gudana. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China