Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwamitin tsaron MDD na fatan kara maida hankali ga batutuwan yaki da ta'addanci a watan Agusta
2020-08-04 14:54:51        cri
Wakilin dindindin na kasar Indonesia a MDD, kuma jagoran kwamitin tsaron majalissar na watan Agustar nan Mr. Dian Triansyah Djani, ya ce MDD na fatan kara rubanya kokarin ta, game da tattauna batutuwan da suka jibanci yaki da ta'addanci cikin wannan wata.

Mr. Djani, ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai, biyowa bayan gabatar da rahoton aiki da kwamitin tsaron ya fitar a jiya Litinin. Jami'in ya kara da cewa, kwamitin tsaron zai kira taron ministoci a ranar 6 ga watan nan, domin gudanar da muhawara game da alakar dake tsakanin akidun ta'addanci, da kungiyoyin kasa da kasa na masu aikata muggan laifuka.

Ya ce za kuma a yi karin haske game da wannan muhimmin batu, yayin gabatar da rahoton shekaru biyu-biyu na babban sakataren MDD, game da barazanar da kungiyar IS da ISIL ko Da'esh suke haifarwa a Iraqi, a ranar 24 ga watan na Agusta. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China