Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta zartar da kudiri kan rawar matasa ga shirin zaman lafiya da tsaro
2020-07-15 11:07:39        cri
Kwamitin sulhun MDD ya zartar da kudiri a ranar Talata don bunkasa rawar da matasa za su taka ga shirin wanzar da zaman lafiya da tsaro.

Kudurin mai lamba 2535 ya samu amincewar mambobin kwamitin sulhun MDDr 15, inda suka bukaci dukkan masu ruwa da tsaki da su duba yiwuwar amfani da dukkan hanyoyin shigar da matasa aikin kandagarkin hana tashe-tashen hankula, da gina zaman lafiya, domin tabbatar da ingantattun hanyoyi mafiya dacewa na shigar da matasa domin a dama da su a shirye-shiryen tabbatar da zaman lafiya da tsaro. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China