Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 11 sun jikkata yayin wata saukar gaggawa da wani jirgin saman MDD ya yi a Mali
2020-08-04 10:45:22        cri
Wani jirgin saman MDD ya yi saukar gaggawa, inda ya sauka daga kan titin jirgi, da safiyar jiya Litinin a birnin Gao dake arewacin kasar Mali, inda aka jibge dakarun MDD.

Wata sanarwa da shirin wanzar da zaman lafiya na MDD a Mali (MINUSMA) ya fitar, ta ce wani jirgin saman shirin da ya tashi daga Bamako dauke da fasinjoji 11, ya yi saukar gaggawa a filin jirgin saman Gao, tana mai cewa daya daga cikin tawagar jirgin ya ji mummunan rauni, yayin da raunin da sauran mutanen 10 suka ji, bai yi tsanani ba.

Bisa hotunan da aka dauka a wurin, jirgin Antonov An-72 da aka yi wa fenti da tambarin MDD, ya lalace sosai.

Shirin na MINUSMA, ya ce za a gudanar da bincike nan bada dadewa ba domin tantance musabbabin lamarin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China