Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin na adawa da mulkin kama karya da neman iko
2020-07-25 16:14:28        cri

Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, Zhang Jun, ya shaidawa kwamitin sulhu na majalisar cewa, kasar Sin na matukar adawa da mulkin kama karya da neman iko.

Zhang Jun, ya shawaidawa wani taron muhawara na kwamitin kan Sauyin yanayi da Tsaro da ya gudana jiya ta kafar bidiyo cewa, idan aka duba yadda duniya take tafiya a yanzu, za a ga yadda dabi'un wasu kasashe na rashin sanin ya kamata da daukar ra'ayi na kashin kai da kuma cin zali, ke haifar da illa. Ya ce idan aka tafi a haka, ba tare da an yi wa tufkar hanci ba, za a rasa aminci da daidaito da adalci da kiyaye dokoki tsakanin kasa da kasa, lamarin da zai jefa duniya cikin tashin hankali. Yana mai cewa, dole ne su goyi bayan juna don yaki da wadancan dabi'u.

Bugu da kari, ya ce duk yadda duniya za ta sauya, kasar Sin za ta ci gaba da goyon bayan tsarin huldar kasa da kasa da tabbatar da adalci da daukaka dokokin kasa da kasa da kuma adawa da mulkin kama karya da cin zali da nuna iko da fifiko. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China