Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Samar da kariya ga mutane miliyan 1.8 da suka kauracewa gidajensu a Najeriya babban abin damuwa ne ga MDD
2020-07-30 09:52:52        cri
Yayin da ake samun tabarbarewa al'amurran tsaro a arewa maso gabashin Najeriya, MDD ta ce bayar da kariya ga fararen hula miliyan 1.8 da suka kauracewa muhallanci babban aiki ne a gaban MDD.

A cewar Farhan Haq, mataimakin kakakin babban sakataren MDDr Antonio Guterres, lalacewar yanayin tsaron yana matukar shafar ayyukan jami'an ba da agaji, yayin da aka kashe ma'aikatan agajin uku, sannan aka lalata jirgin helikwafta na MDD a wata musayar wuta da aka yi a jahar Borno a farkon wannan wata.

Haq ya fadawa taron manema labarai ta kafar bidiyo cewa, bayar da kariya ga fararen hula babban abin damuwa ne ga MDD.

Ya zuwa yanzu yawan kudin da aka samu ya kasa da kashi 30 bisa 100 daga cikin dalar Amurka fiye da biliyan daya da ake bukata domin gudanar da aikin jin kai a shekarar 2020. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China