Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban jami'in MDD ya bukaci a samar da sabuwar yarjejeniyar al'ummar kasa da kasa domin magance matsalar rashin daidaito
2020-07-19 17:05:04        cri
Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya bukaci a samar da sabuwar yarjejeniya a tsakanin al'umma da kuma sabuwar yarjejeniyar kasa da kasa domin shawo kan matsalolin rashin daidaito a tsakanin al'umma a fadin duniya.

Cutar COVID-19 bala'i ne da ya shafi dukkan bil adama. Amma kuma ya samar da wata dama ga al'ummar wannan karni ta yadda za'a kara gina tsarin daidaito da ci gaba mai dorewa a duniya, Guterres ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar ta taron Nelson Mandela na shekara shekara, wanda aka gabatar ta kafar bidiyo. Ya ce matakan yaki da annobar, da karuwar rashin gamsuwa game da yaki da cutar, tilas ne ya kasance bisa ga sabon tsarin yarjejeniyar al'umma da sabuwar yarjejeniyar kasa da kasa wacce za ta samar da damammaki na bai daya ga kowa da mutunta hakkoki da 'yancin kowa.

Sabon tsarin yarjejeniya a tsakanin al'umma zai baiwa matasa damar yin rayuwa cikin mutunci, zai baiwa mata damar samun makoma da kuma damammki kamar takwarorinsu maza, kuma hakan zai baiwa marasa lafiya kariya, da marasa galihu, da kananan kabilu daga dukkan fannoni.

Sai dai kuma, Guterres ya ce, tsarin siyasar duniya da na tattalin arziki ba'a tafiyar da su bisa ga bangarorin da al'umma suka fi bukata, kamar bangaren kiwon lafiya, yaki da sauyin yanayi, samar da dauwwamammen ci gaba, da tabbatar da zaman lafiya. Annobar COVID-19 ta bankado wasu abubuwa na cikin gida inda ta banbance tsakanin bukata ta kashin kai da bukatun bai daya, da kuma babban gibi a tsarin gwamnati da hakikanin manufofin ci gaba. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China