Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwamitin sulhun MDD ya nuna damuwa kan halin da yammacin Afirka da Sahel suke ciki
2020-07-29 10:47:52        cri
Kwamitin sulhu na MDD ya bayyana damuwa matuka, game da yadda yanayin tsaro da na jin kai ke kara tabarbarewa a yankin Sahel da tafkin Chadi da ma kalubalen tsaro a yammacin Afirka.

A wata sanarwar shugaba da ya fitar, kwamitin ya yi kira ga kasashe, yankuna da duniya baki daya, da su taimakawa kasashen dake shiyyar, ta yadda za su magance kalubaloli na zaman lafiya da tsaro da suke fuskanta.

Kwamitin ya kuma bayyana damuwa, game da yanayin jin kai a yankin, musamman yadda ake tilastawa mutane barin matsugunansu, da kangin talauci, da rashin daidaito da tashin hankali, ciki har da cin zarafi masu nasaba da yin lalata da kuma jinsi.

A don haka, kwamitin ya yi kira da a ba da damar kai kayayyakin agaji da na lafiya ga mutanen da suke matukar bukata ba tare da wata matsala ba, ciki har da ba da damar kaiwa ga wadanda suka tsira daga cin zarafi na lalata a lokacin tashin hankali da ma bayan yanayi na tashin hankali.

Kwamitin sulhun ya kuma bayyana damuwa, kan yadda annobar COVID-19 ke ci gaba da yin tasiri a yankin, da yadda take shafar ci gaba, da dagula yanayin jin kai da yadda take shafar mata da 'yan mata da kananan yara da 'yan gudun hijira, wadanda suka kauracewa muhallansu da tsoffi gami da mutane masu rauni a cikin al'umma. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China