Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Taimakawa masu fama da talauci ta hanyar koyar da dabarun dafa abinci
2020-07-16 16:47:21        cri

Hadin gwiwa a tsakanin sassan yammaci da gabashin kasar Sin a kokarin kawar ta talauci, wata hanya ce ta musamman da aka fidda bisa tsarin gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin, domin gina al'umma mai matsakaicin wadata. Bisa wannan shirin, birnin Fuoshan na lardin Guangdong ya dauki nauyin taimakawa yankin Liangshan mai cin gashin kansa na kabilar Yi dake lardin Sichuan. A shekarar 2018, yankin Shunde na birnin Fuoshan ya kwasa kwasai na koyar da fasahohin dafa abinci domin taimaka wa masu fama da talauci, cikin shekaru 2 da suka gabata, an yi nasarar horas da mutane sama da dari 3, wadanda suka koyo fasahohin dafa abinci masu kyau.

Lu Yuxian yana koyon fasahohin dafa abinci a sashen koyon fasahar aikin kuku na kwalejin koyar da fasahohin sana'a na birnin Shunde na lardin Guangdong, a wayar salularsa, ya rubuta fasahohin dafa abinci iri daban daban. Ya ce, a tsawon rabin wata da yake koyon fasahohi a nan, ya koyi fasahohin dafa nau'o'in abinci 70. Kana, a cikin ajinsa, gaba daya, akwai dalibai guda 30, kuma dalibi mafi karami shi ne mai shekaru 18, yayin da dalibi mafi tsufa, shi ne mai shekaru 49, akwai kuma mutane 5 da suka fito daga gidaje masu fama da talauci.

Shugaban sashen koyon fasahar aikin kuku-kuku Chen Jian ya shirya bikin fara sabon zangon karatu ga dalibai, kuma wannan shi ne karo na 9 da aka marabci dalibai daga yankin Daliangshan. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China