Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kawar da talauci ta hanyar noman furen Daylily
2020-07-17 13:53:41        cri

Yankin Yunzhou na birnin Datong dake lardin Shanxi na kasar Sin yana da tarihin noman furen Daylily na sama da shekaru 600, lamarin da ya sa ake kiran yankin "garin furen Daylily".

Kayayyakin da aka yi da furen Daylily na birnin Datong sun samu karbuwa sosai a kasuwannin kasar Sin, wannan ya sa a lokacin girbin furannin Daylily na bana, gwamnatin birnin ta taimakawa manoman wajen girbin furannin Daylily, ta kuma dauki masu fama da talauci wannan aiki don taimaka musu a aikin girbin furannin.

A shekarar 2011, yankin Yunzhou ya mai da sana'ar samar da furannin Daylily a matsayin wani ginshiki na tattalin arzikin wurin, sa'an nan, ya kafa kungiyar furen Daylily, tare da gabatar da manufofin raya sana'ar guda 21, da kuma zuba jari na yuan miliyan 410 a wannan aiki.

A watan Mayu na bana, yayin ziyararsa a gonakin noman furen Daylily na birnin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi fatan ganin furen Daylily ya zama "furen da zai samar da wadata" ga al'ummar wurin.

Yanzu, fadin gonakin da ake noman furen Daylily a yankin Yunzhou na birnin Datong ya kai sama da muraba'in kilomita 113, kuma kudaden da suke samar wa a ko wace shekara ya kai yuan miliyan dari 7, lamarin da ya sa ko wane manomi ya kan sami karin kudin shiga da ya kai yuan dubu 5 a ko wace shekara, baya ga taimakawa wajen fitar da magidanta kimanin dubu 15 daga kangin talauci. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China