Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: COVID-19 na kara yaduwa a kudu da hamadar Afirka
2020-07-21 09:51:10        cri

Babban daraktan ayyukan gaggawa na hukumar lafiya ta duniya WHO Dr. Michael Ryan, ya ce cutar numfashi ta COVID-19 na kara yaduwa a sassan yankunan kudu da hamadar Saharar Afirka.

Dr. Ryan ya bayyana hakan ne a jiya Litinin, yayin taron manema labarai da ya gudana, yana mai cewa kasashe irin Afirka ta kudu, na kan gaba wajen samun karuwar masu harbuwa da cutar, inda ya zuwa Litinin kasar ta kai matsayi na 5 a duniya a wannan fanni.

Alkaluman WHOn sun nuna cewa, Afirka ta kudun ta samar da kaso 60 bisa dari na daukacin yawan masu harbuwa da wannan cuta a Afirka. Da fari yankunan mawadata ne suka fara fuskantar bazuwar annobar, kafin daga bisani ta bazu zuwa yankunan matalauta, ta kuma karade daukacin sassan al'ummar kasar.

Bisa jimilla, mutane 597,223 ne suka kamu da cutar COVID-19 a nahiyar, ciki hadda mutane 9,691 da ta hallaka, kamar dai yadda alkaluman hukumar WHO suka tabbatar. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China