Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban cibiyar dakile yaduwar cututtukan Amurka: Amurka ba ta fita daga mawuyacin hali ba
2020-07-15 10:43:23        cri

Jiya Laraba, shugaban cibiyar kandagarki da dakile yaduwar cututtuka na kasar Amurka Robert Redfield ya bayyana cewa, a halin yanzu, cutar numfashi ta COVID-19 tana ci gaba da yaduwa a sassan kasar Amurka, duk da cewa yanayin hana yaduwar cutar ya kyautata idan aka kwatanta da lokacin bazara, amma har yanzu kasar ba ta fita daga mawuyacin hali ba tukuna. Ya kara da cewa, Amurka ta sami ci gaba kan wannan aiki, amma, akwai doguwar hanya dake gaban kasar ta fuskar dakile yaduwar annoba.

Bisa sabuwar kididdigar da jami'ar Johns Hopkins ta kasar ta fidda, ya zuwa karfe 1 da kwata na ranar 14 ga wata, gaba daya, an tabbatar da mutane 3,374,654 da suka kamu da cutar COVID-19 a kasar, sa'an nan, mutane 135,984 sun rasu sakamakon cutar. Kasar Amurka ita ce ta fi fama da cutar numfashi ta COVID-19 a duk fadin duniya. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China