Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jaridar The Washington Post: Kuskuren da Amurka ta yi wajen dakile annobar COVID-19, "Hargitsi mai ban mamaki ne na duniya"
2020-07-21 13:46:21        cri

Tun daga watan Yuli, gwamnatin kasar Amurka ta dauki jerin matakai, wadanda suka kara tsananta yanayin da kasar ke ciki na tinkarar annobar numfashi ta COVID-19, har ma da illata ayyukan dakile annobar na daukacin duniya.

A ranar 20 ga watan Yuli bisa agogon wurin, jaridar The Washington Post ta kasar Amurka, ta ba da rahoto mai taken "Hargitsi mai ban mamaki na duniya: amsar da Amurka ta gabatar kan annobar COVID-19". Rahoton ya ce, a cikin 'yan watannin da suka gabata da ake tinkarar cutar, wasu kasashe da dama sun cimma nasarar shawo kan annobar, amma, a kasar Amurka an gaza hana yaduwar annobar, jihohi daban daban na kasar ba su hada kai sosai wajen dakile annobar ba, a maimakon haka, ana nuna gaba da kawo baraka a fannin siyasa.

Rahoton ya nuna a bayyane cewa, sakacin da gwamnatin kasar Amurka ta yi kan ayyukan dakile annobar yana da ban mamaki. Kwararru a fannin kiwon lafiyar jama'a sun bayyana cewa, kuskure ne mafi tsanani da gwamnatin Amurka ta yi kan ayyukan tinkarar annobar, shi ne a yayin da ake samun saurin yaduwar annobar, tana dora muhimmanci kan sake farfadowar tattalin arziki cikin gaggawa.

Jaridar The Hill ta kasar Amurka ta ba da labarin cewa, gwamnatin Amurka ta bukaci asibitocin kasar su gabatar da bayanai game da annobar COVID-19 ga hukumar kula da kiwon lafiya da ba da hidima ga jama'a ta tarayyar kasar kai tsaye, maimakon ta hannun cibiyar kula da cututtuka ta kasar kamar yadda ake yi a da.

Tsohon daraktan cibiyar Richard Besser ya bayyana cewa, wannan mataki da gwamnatin tarayyar kasar ta dauka, ja baya ne da kasar ta kara yi wajen dakile annobar.

Jaridar The Washington Post ta ba da sharhin cewa, a karkashin jagorancin gwamnatin Donald Trump, Amurkawa masu yawa suna ganin cewa, masana da kwararru a fannin kimiyya da muhimman kafofin watsa labaru, sun yi korafi kan tsanantar yanayin da kasar ke ciki game da tinkarar annobar, har ma sun tsara wasu labaran karya kan annobar. Kauracewar da aka yi kan masana da kwararru, tana sauyawa zuwa matsayin makirci, wanda kuma ya kasance wani sashe ne na ajandar siyasar gwamnatin Amurkar. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China