Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Batun rufe ofishin jakadancin Sin dake Houston zai haifar da koma bayan dangantaka
2020-07-23 17:09:08        cri

A ci gaba da daukar matakan matsawa kasar Sin lamba da mahukuntan Amurka ke yi, a baya bayan nan, ba zato ba tsammani gwamnatin shugaba Trump ta ba da umarnin rufe karamin ofishin jakadancin Sin dake birnin Houston na Amurkar, matakin da masharhanta da dama ke kallo, a matsayin wata tsokana ta siyasa da Amurka ta bijiro da ita, da nufin muzgunawa kasar ta Sin.

Tuni dai mahukuntan Sin suka yi matukar Allah wadai da wannan mataki, suna masu bayyana shi a matsayin karya doka, da ka iya haifar da karin tsamin dangantaka tsakanin manyan kasashen guda biyu.

Kamar dai sauran lokuta, Amurka na fakewa da wasu dalilai marasa tushe, wajen daukar matakan dake keta ka'idojin cudanyar kasa da kasa, musamman kan kasar Sin. A wannan lokaci ma dai mahukuntan Amurka sun alakanta rufe karamin ofishin jakadancin kasar Sin dake birnin Houston, da zargin cewa, ana amfani da ofishin wajen yiwa kasar leken asiri.

To sai dai kuma, umarnin dakatar da dukkanin ayyukan wannan ofis na jakadanci cikin kankanen lokaci ya tada kura, inda masu fashin baki da dama, ke kallon lamarin a matsayin ci gaba da Amurka ke yi da siyasantar da dukkanin sassan dangantakarta da kasar Sin, duk da cewa hakan ba zai haifarwa Amurkan, da ma duniya baki daya da mai ido ba.

Sanin kowa ne cewa, dangantakar kasashe na ginuwa ne bisa tushen mutuntawa, da yarda da juna, da kuma tattaunawa idan an samu sabani, amma irin wadannan matakai da Amurka ke dauka, na barazana, da matsin lamba, da keta dokoki, da ka'idojin cudanyar kasashen duniya, ba su taba warware wani sabani ba. A maimakon hakan, irin wadannan matakai ba abun da za su haifar, sai mayar da hannu agogo baya.

A baya bayan nan, mun ga yadda jami'an gwamnatin Amurka, da 'yan siyasar kasar ke kara matsa kaimi, wajen sukar manufofin kasar Sin na cikin gida, matakin da ya kai Amurkan ga kakabawa wasu jami'ai, da kamfanoni, da ma 'yan jam'iyyar kwaminis mai mulkin Sin takunkumi, na hana ba su VISAr shiga Amurka. Kafin hakan mun ga yadda Amurka ta rika kokarin dorawa Sin alhakin yaduwar cutar COVID-19 a sassan duniya. Bayan ga batun mayar da WHO 'yar amshin shata da Amurkan ta zargi Sin da aikatawa. Dadin dadawa, Amurka ta zuga kawayen ta da su kauracewa hulda da kamfanin fasaha na Huawei, tana mai cewa kamfanin na yiwa kasar Sin wasu ayyuka ne na sirri. Kana Amurka ta yi yunkurin shafawa kasar Sin kashin kaji ta hanyar ayyana mambobin jam'iyyar kwaminis ta Sin da 'yan ta'adda.

Amurka ta sha tsoma baki a harkokin da suka shafi yankin musamman na Hong Kong, da yunkurin kulla alakar kai tsaye, da jagororin yankin Taiwan, da yin suka game da manufofin tsaro da ake aiwatarwa a jihar Xinjiang ta Uyghur mai cin gashin kanta, duka dai da nufin bata sunan kasar Sin a idon duniya.

Wadannan misalai ne kadan, cikin tarin matakai da Amurka ke dauka na matsawa Sin lamba, wanda hakan a cewar masana da kwararru da dama, dabara ce ta dakushe tasiri, da ci gaban kasar Sin. To sai dai kuma, masu fashin baki da dama na ganin hakan ba zai takawa kasar Sin birki, a hanyarta ta kara samun wadata, da fadada cudanyar ta da sauran sassan duniya ba.

A hannu guda, kamar yadda aka gani a baya, Sin a shirye take za ta mayar da martini bisa doka, a kuma lokuta mafiya dacewa kan irin wadannan matakan da Amurka ke dauka kanta.

Fatan dai shi ne, tun da wuri Amurka za ta fahimci kurakuranta, ta dakatar da wadannan matakai marasa tushe da take aiwatarwa, ta kuma gane cewa "zama lafiya ya fi zama dan sarki". Kuma babu wata kasa da za ta samu cimma burinta, ba tare da hadin kai, da goyon bayan sauran sassan duniya ba. (Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China