Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dalilin Da Ya Sa Aka Ce, Gwamnatin Trump Ta Taimaka Kasar Sin
2020-06-22 16:00:12        cri
Ko shakka babu, gwamnatin kasar Amurka dake karkashin jagorancin Donald Trump ita ce gwamnatin da ta fi bata ran kasar Sin, bayan shekarar 1971 da aka fara kokarin daidaita dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasar Amurka. Ta tada wani yakin cinikin dake tsakaninta da kasar Sin, wanda ya haddasa hasara ga tattalin arzikin kasar Sin, ta kuma kakaba wa kasar Sin takunkumi ta fuskar fitar da fasahohi. Ta kuma dauki matakai iri daban daban domin hana bunkasuwar kamfanin Huawei. Kana, abu mafi bata ran al'ummomin kasar Sin shi ne, matakin da gwamnatin kasar Amurka ta dauka wajen tsare jami'ar kamfanin Huawei, wato Meng Wanzhou, inda ta aiwatar da dokar kasarta kan mutumiyar kasar Sin, lamarin da ya fusata al'ummomin Sin kwarai da gaske.

Amma, idan aka duba wannan batu ta wani bangare na daban, kamar yadda shugabannin kasar Sin su kan yi bisa manyan tsare-tsare, mai yiyuwa ne, za a ce, gwamnatin kasar Amurka dake karkashin jagorancin Donald Trump ta ba da taimako ga kasar Sin. A hakika dai, gwamnatin kasar Amurka a karkashin jagorancin Trump ba ta tsara manufofi da idon basira ba wajen fuskantar ci gaba na bunkasuwar kasar Sin, kuma ba ta ji shawarwarin kwararru yadda ya kamata ba. Gwamnatin Trump ta kasa gina wata kasa mai kwarewa wajen warware harkokin cikin gida da kuma wata kasa mai karfi. Bayan matsalar yaduwar cutar COVID-19 da matsalar George Floyd da suka auku a kasar Amurka, sunan kasar ya baci a duk fadin duniya. Lamarin da ya sa, aka daga matsayin kasar Sin cikin kasa da kasa, a halin yanzu, ana ganin cewa, kasar Sin ta fi karfi a duk fadin duniya.

Kuma, abu mai muhimmanci shi ne, jami'an diflomasiyyar kasar Amurka George Frost Kennan, ya taba jaddada cewa, ya kamata kasar Amurka ta kara abota da kawancenta. Amma, gwamnatin Trump ta bata dangantakar dake tsakaninta da abokanta da kuma kawayenta. Kuma, abin da ya bata ran al'ummomin kasa da kasa shi ne, a lokacin da kasashen duniya, musamman ma kasashen Afirka suke bukatar taimakon hukumar WHO, kasar Amurka ta janye jiki daga hukumar, lalle ba ta dauki alhakinta yadda ya kamata ba.

Bugu da kari, bai kamata gwamnatin kasar Amurka ta zagi kasar Sin ba, ba wanda ya taba zagin kasar Sin kamar yadda Donald Trump ya yi. Mai iyuwa, irin zargin da Trump ya yi wa gwamnatin kasar Sin, zai bata imanin al'ummomin kasar Sin kan gwamnatinsu, amma, bisa kididdigar da aka yi, gwamnatin kasar Sin ita ce gwamnati mafi samun amincewar al'ummomin kasa, har adadin ya kai 90%. Wannan ba abin mamaki ba ne, sabo da, a ganin galibin mutanen Sin, bunkasuwar tattalin arziki da kyautatuwar zaman takewar al'umma da suka samu cikin shekaru 40 da suka gabata, sun zama mafi kyau cikin shekaru 4000 da suka gabata. (Mai Fassara: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China