Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bayanin Jam'iyyar Republic Ta Amurka Tamkar Kalaman Wasa Ne Mai Ban Dariya
2020-04-27 17:00:27        cri
Kwanan baya, an wallafa wata takardar bayanin da kwamitin majalisar dattawa ta jam'iyyar Republic ya samar ga hukumomin zabe a shafin intanet na Politico, inda a ciki aka bayyana tsara wasu dabaru ga 'yan takarar jam'iyyar, kan yadda za su fuskanci zargin da al'ummomin kasar suke yi musu ta hanyar cin zarafin kasar Sin.

Takardar bayanin ta gabatar da dabaru guda uku, na farko shi ne, yada jita-jitar cewa, wai Sin, ta boye labaran cutar numfashi ta COVID-19, wanda ya haddasa yaduwar annobar. Na biyu shi ne, zargin 'yan takarar jam'iyyar dimokuradiyya cewar, sun nuna tausayi wanda bai kamata ba ga kasar Sin. Na uku shi ne, jam'iyyar Republic za ta sanye takunkumi kan kasar Sin sabo da Sin din ce ta haddasa yaduwar wannan annoba.

Kwanan baya, dan kasar Amurka Max Blumenthal, marubucin kafar yada labarai ta "Gray Zone" mai zaman kansa dake kasar Amurka, ya yi bayani kan yadda kasar Amurka ke dukufa wajen bata sunan kasar Sin, inda ya ce, da farko, gwamnatin kasar za ta gabatar da wasu labarai ga kafofin watsa labarai, sa'an nan, kafofin watsa labaran kasar za su gabatar da labaran ga al'ummomin kasar, daga bisani kuma, 'yan siyasan kasar za su yi kira da a dauki sabbin matakai domin kakabawa kasar Sin takunkumi.

A halin yanzu, kasar Amurka tana fama da matsalar yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 cikin sauri, don haka ya kamata ta daina cin zarafin kasar Sin, in ba haka ba, za ta haddasa babbar illa ga al'ummomin kasar ta. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China