![]() |
|
2020-07-20 21:24:22 cri |
Sanin kowa ne cewa, fahimta da mutunta juna suna da matukar muhimmanci wajen yin mu'amala a tsakanin kasa da kasa. Halin musamman mafi muhimmanci da kasar Sin ke da shi shi ne Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ce ke mulkin kasar, lamarin da tun tuni kasashen Sin da Amurka suka kulla huldar jakadanci a tsakaninsu, kuma Amurka ta san da haka sosai. Amma yanzu wasu 'yan siyasan Amurka sun kawar da kai daga muhimman ka'idojin kulla huldar diplomasiyya a tsakanin manyan kasashe da kuma raya hulda a tsakanin kasa da kasa, sun nuna kiyayya ga JKS. Hakika sun nuna kiyayya ga jama'ar Sin da yawansu ya kai kashi 1 cikin kashi 5 na yawan al'ummar duniya. Wannan rashin hankali ne da ma rashin basira.
Yanzu haka kasashen duniya suna bin hanyar samun ci gaba cikin lumana. Tun tuni an yi watsi da tunanin McCarthyism, inda aka nuna kiyayya ga tunanin Kwaminisanci. 'Yan siyasan Amurka, wadanda suke kokarin dawo da tunanin McCarthyism, idan ba su gaggauta dakatar da abin da suke ba, tabbas ba za su yi nasara ba. (Tasallah Yuan)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China