Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mike Pompeo Ya Sake Yin Karya Da Sunan Addini Domin Shafa Wa Kasar Sin Kashin Kaji
2020-06-12 21:16:12        cri
Kwanan baya, majalisar harkokin wajen kasar Amurka ta gabatar da rahotonta na shekarar 2019 dangane da 'yancin bin addini a duniya, inda ta bata sunan kasar Sin ta fuskar manufofinta na addini. Kana a yayin taron manema labaru da aka yi a wannan rana, Mike Pompeo, sakataren harkokin wajen Amurak ya sake yin karyar cewa, kasar Sin ta danne harkokin addini.

Yayin da gwamnatin Amurka take gallazawa masu zanga-zangar kin amincewa da wariya launin fata a cikin gida, ta kuma matsa wa wasu kasashe lamba da sanya musu takunkumi, lamarin da ya tsananta kiyayya a tsakanin masu bin addini daban daban. Yaushe Pompeo ya zama mai koyar da harkokin kiyaye hakkin dan Adam? Ya yi karya tare da yin sukar manufofin sauran kasashe ta fuskar addini. Abin da ya yi, abin dariya ne.

Mutunta da kiyaye 'yancin bin addini, babbar manufa ce da kasar Sin take bi. Alkaluma sun nuna cewa, yanzu akwai mutane kusan miliyan dari 2 a kasar Sin, tare da masu aikin addini fiye da dubu 380 da kungiyoyin addinai 5500, da wuraren addinai da aka yi rajista bisa doka fiye da dubu 140. A jihar Xinjiang ma, wadda ta fi jawo hankalin 'yan siyasan Amurka, akwai wuraren addini fiye da dubu 28, da masu aikin addini kusan dubu 30. Akwai masallacin dake iya daukar musulmai 530 a lokaci guda, yayin da yawan masallatai da ke Amurka bai kai kashi 1 cikin kashi 10 ba bisa jimillar masallatai dake jihar ta Xinjiang.

Amurkawa da dama sun rasa rayukansu sakamakon annobar cutar numfashi ta COVID-19 baya ga matsalar wariyar al'umma a Amurka. Ko Mike Pompeo da sauran irinsa wadanda suke bautawa Ubangiji ba za su amsa laifinsu na haddasa rashin jituwa, da keta hakkin dan Adam da 'yancin kai a gabansa? (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China