![]() |
|
2020-07-19 17:38:50 cri |
Kowa ya gani da idonsa cewa, Mike Pompeo da wasu 'yan siyasar Amurka suna yunkurin matsawa kasar Sin lamba ta hanyar lalata zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin tekun kudancin kasar Sin. Sun yi watsi da alkawarin da gwamnatin Amurka ta yi a baya, wato gwamnatin Amurka ba ta da matsayi kan batun tekun kudancin kasar Sin. Mike Pompeo da takwarorinsa sun runbaya aniyarsu don ganin an nuna kiyayya tsakanin kasa da kasa. Ba su da idon basira, da da'a da ma aminci.
Duk da haka kasashe mambobin kungiyar ASEAN sun fahimci cewa, wadannan 'yan siyasar Amurka dake mayar da Amurka a gaban komai ba su kula da muradun sauran kasashe, suna amfani da kasashe mambobin kungiyar ASEAN don neman samun moriyar siyasa ne kawai. Duk abin da Mike Pompeo da 'yan siyasan Amurka suka yi ba zai sauya aniyar kasar Sin na kiyaye ikon mulkin kasa, da tsaron kasa da ci gaban kasa ba, kana ba zai lalata buri da kokarin da kasashen dake yankin tekun kudancin kasar Sin suke yi wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin tare ba.
Kasar Sin da kasashe mambobin kungiyar ASEAN suna da basira da kwarewa wajen daidaita batunsu. Ba su bukata kuma ba su yarda da wasu kasashen da ba na wannan yanki ba su tsoma baki cikin batun yankin. Ya fi kyau 'yan siyasan Amurka su gaggauta juya hankalinsu kan yaki da annobar COVID-19 a gida, su dakatar da rura wuta a duniya. Tarihi zai nuna cewa, yunkurin Mike Pompeo da takwarorinsu zai ci tura a karshe a tekun kudancin kasar Sin. (Tasallah Yuan)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China