![]() |
|
2020-06-11 20:40:43 cri |
Cikin kwanaki 10 da suka gabata, mutuwar wani Ba'amurke bakar fata mai suna George Floyd ta haifar da gagarumar zanga-zangar neman kare hakkin dan Adam a Amurka baki daya. Amma abin bakin ciki shi ne wasu 'yan siyasan Amurka da kafofin yada labaru ba su yi nadaman faruwar lamarin ba, maimakon haka ma, sai suka ci gaba da rura wutar rikicin wariyar al'umma, wanda yake illata hadin kan al'ummomin Amurka.
Abun da yake faruwa a Amurka ya sake sanya kasashen duniya kara sanin cewa, wadancan 'yan siyasan Amurka da kullum suke kiran kansu masu rajin kare hakkin dan Adam su ne wadanda suka haifar da matsalar hakkin dan Adam. A matsayinsa na babban jakadan Amurka, sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo ya kan fake da sunan "demokiradiya da hakkin dan-Adam" yana sokar wasu kasashe, amma bai ce kome ba kan zanga-zangar kin amincewa da wariyar al'umma dake faruwa a cikin gida Amurka ba.
Yanzu kowa ya san cewa, ainihin tunanin wasu 'yan siyasan Amurka dangane da kiyaye hakkin dan Adam shi ne keta hakkin dan Adam don biyan bukatunsu. Shin wadancan masu rajin kare hakkin dan Adam ba su ji kunyar fadan "'yanci" da "dimokuradiyya"? Lokaci ya yi da za a kawo karshen nuna fuska biyu kan batun kiyaye hakkin dan Adam. (Tasallah Yuan)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China