Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta dauki kwararan matakan tabbatar da bunkasar tattalin arziki a yayin da ta samu nasarar shawo kan annobar COVID-19
2020-07-22 17:15:08        cri

A jiya Talata, an shirya wani taron kara wa juna sani tsakanin shugabannin kasar Sin da 'yan kasuwar kasar, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci a kara kokari don ganin kasuwa ta yi halinta da ma bunkasa harkokin kasuwanci.

Xi ya kara yin kira da a kara zage damtse, ta yadda sha'anin kasuwanci zai taka muhimmiyar rawa tare da samun gagarumin ci gaba.

A yayin da har yanzu wasu sassa na duniya ke fama da annobar COVID-19, gwamnatin kasar Sin ta shirya wannan taro, yana da muhimmanci matuka ga kokarin farfado da kuma bunkasa tattalin arzikin kasar, har ma duk duniya.

Yanzu ku san dukkan fannoni sun dawo bakin aikin a kasar Sin, abin da ke nuna cewa, matakan da kasar ta dauka na yaki da cutar, sun yi matukar tasiri. Wannan ne ma ya sa, a kwanakin baya hukumar kididdiga ta kasar Sin (NBS) ta sanar da cewa, alkaluman GDPn kasar ya karu a rubu'i na biyu na shekarar bana, karuwar kaso 3.2 cikin 100 kan makamancin lokaci na bara.

A cewar alkaluman hukumar, a watanni 6 na farkon bana, GDPn kasar ya kai Yuan tiriliyan 45.66, kwatankwacin dala tiriliyan 6.53, raguwar kaso 1.6 cikin 100 kan na bara, hakan ya faru ne sakamakon tasirin COVID-19.

Sai dai alkaluman da hukumar ta fitar, sun nuna yadda kasuwar samar da ayyukan yi ta kasar Sin ta dan inganta a watan Yuni, inda rashin aikin yi a yankunan biranen kasar ya tsaya a kaso 5.7 cikin 100, wato kasa da kaso 0.2 cikin 100 kan na watan da ya gabata.

Sakamakon manufar kasar Sin na kara bude kofarta ga ketare, da sabbin manufofi da matakai na inganta yanayin kasuwanci da kara sakarwa kasuwa mara don samun ci gaba, ciki har da saukaka ka'idoji na gina ayyuka da harkokin kudi da yanayin kafa masana'antu da samar da yanayin cinikayya da zuba jari ga masu jarin waje, ya sa kamfanonin ketare na rige-rigen zuba jari da gudanar da harkokinsu na kasuwanci a kasar Sin.

Sauran fannonin sun hada da samar da guraben ayyukan yi da kafa masana'antu, da inganta hidimomin kasuwanci da inganta matakan yanayin kasuwanci na dogon lokaci.

Abin farin ciki shi ne, wadannan ka'idoji sun bayyana bukatar rage hanyoyin shiga kasuwa, da samar da hidimomin kiwon lafiya da bangarorin wasanni.

Haka kuma, an bukaci cire dukkan wasu shingaye dake hana ruwa gudu a bangaren gudanarwa da zuba jari ga masu sha'awar zuba jari na ketare da ma kamfanonin ketare. Da ma sai an zubar da ruwa a kasa kafin a taka damshi.

Sai dai, duk da kalubale da matsin lamba gami da rashin tabbas da kasar Sin take fuskanta wajen tabbatar da ci gaban cinikin waje. A shirye kasar take wajen tunkarar duk wata barazana daga waje cikin dogon lokaci. Kana tana da aniya da kwarewa wajen ci gaba da jawo jarin waje, tare da samar wa duniya damar ci gaba, ganin irin jerin matakan da take dauka na raya tattalin arzikinta. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China