2020-07-17 11:08:13 cri |
Da farko a jiyan, kasar Sin ta fitar da rahoton da ya bayyana karuwar tattalin arzikinta da kaso 3.2 a cikin rubu'i na 2 na bana.
Jaridar ta ce, harkokin kasuwanci na kasar Sin sun cike gibin dake akwai wajen samar da kayayyaki a duniya, tare da fadada fitar da kayayyaki, saboda kamfanonin kasar sun fara aiki kafin na sauran kasashen duniya dake fitar da kayayyaki.
Rahoton da jaridar ta wallafa mai taken "Da alamu tattalin arzikin kasar Sin ya farfado, amma har yanzu akwai kalubale" ya kuma bayyana cewa, akwai banbanci sosai ga kamfanonin kasashen waje dake aiki a ciki da wajen Sin.
Sai dai, takardar ta ce babbar barazana ga kasar Sin ka iya zama Amurka, inda manyan jami'an kasar da 'yan majalisun dokoki daga dukkan manyan jam'iyyun kasar biyu, ke kara matsawa Sin lamba da kakaba takunkumi kan jami'ai da kamfanonintan, gabanin zaben shugaban Amurka dake tafe cikin watan Nuwamba. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China