Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tattalin arzikin Sin ya haye kalubalen COVID-19
2020-07-17 20:14:37        cri
Tattalin arzikin kasar Sin ya sauya daga halin matsi zuwa na ci gaba, a rubu'i na biyu na shekarar bana. A halin yanzu kuma, fannin na kara farfadowa, bayan matsayin da ya fuskanta a watanni 6 na farkon wannan shekara.

Kafofin watsa labarai da dama na ganin cewa, hakan ya nuna yadda kasar ta samu nasarar shawo kan cutar numfashi ta COVID-19 cikin nasara, kuma alamu na nuna yadda tattalin arzikin na Sin zai kara bunkasa cikin sauri, cikin watanni 6 na karshen shekarar ta bana.

Da take tsokaci game da hakan, mai magana da yawon ma'aikatar harkokin wajen Sin Hua Chunying, ta ce shaidu sun tabbatar cewa, tattalin arzikin Sin ya kai ga jure kalubalen cutar ta COVID-19, kana yanayin ci gaba, da dorewar sa cikin kyakkyawan yanayi a dogon lokaci mai zuwa bai sauya ba.

Hua, wadda ta bayyana hakan a yau Juma'a, yayin taron manema labarai na rana rana da aka saba gudanarwa a nan birnin Beijing, ta ce a halin yanzu, wannan annoba na kara bazuwa a sassan duniya, kuma tasirin ta kan tattalin arzikin duniya har yanzu na fadada, yayin da a daya bangaren shi ma tattalin arzikin Sin ke fuskantar irin na sa kalubale.

To sai dai kuma a cewar ta, Sin a shirye take ta karfafa tsare tsaren manyan fannonin tattalin arzikin ta da hadin gwiwar dukkanin sassa, da karfafa hadin gwiwa a bangaren kandagarki da shawo kan cutar COVID-19, da kara farfado da matakan komawa ayyuka, da sarrafa hajoji.

Sauran fannonin sun hada da hadin gwiwa wajen gina tattalin arzikin duniya a bude, tare da aiwatar da dukkanin matakan da za su ba da damar ingiza tattalin arzikin duniya, ta yadda zai samu fita daga komada cikin gaggawa, ya kuma farfadowa cikin sauri. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China