Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanonin Waje Suna Gaggauta Zuba Jari A Kasar Sin
2020-07-21 21:16:28        cri
A bana, kamfanin kera motoci na Volkswagen na kasar Jamus ya shirya ganawa da abokan cinikinsa wajen zuba kudin EURO fiye da biliyan 4 a kasar Sin. Babban jami'in kamfanin Stephan Wollenstein ya bayyana yayin da yake zantawa da wakilinmu cewa, kara bude kofar kasar Sin zuwa ketare ya samar wa kamfaninsa karin damammaki. Akwai shugabannin manyan kamfanonin kasa da kasa da dama wadanda suke da ra'ayi iri daya da Stephan Wollenstein. Cikin watanni da dama da suka gabata, kamfanonin Qualcomm da Pepsi da dai sauransu sun gaggauta zuba jari a kasar Sin, a kokarin habaka cinikinsu a kasar Sin.

Hukumar kula da harkokin ciniki da bunkasuwa ta MDD wato UNCTAD ta yi hasashen cewa, yawan jarin da 'yan kasuwan waje za su zuba kai tsaye a duniya daga shekarar 2020 zuwa 2021 zai ragu da 30% zuwa 40%, sakamakon barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19. Amma yawan jarin waje da kasar Sin ta yi amfani da shi a zahiri daga watan Afrilu zuwa watan Yuni a bana ya karu da 8.4% bisa makamancin lokaci na shekarar bara, lamarin da ya nuna cewa, ya zuwa yanzu kamfanoni na alla-alla wajen zuba jari a kasar Sin. Dalilan da suka sa haka su ne domin kasar Sin ta raya tattalin arzikinta yadda ya kamata, tana kuma kyautata yanayin kasuwanci, sa'an nan tana ci gaba da kokarin kara bude kofarta ga kasashen ketare.

Yanzu haka annobar tana yaduwa a duniya. Duk da kalubale da matsin lamba gami da rashin tabbas da kasar Sin take fuskanta wajen tabbatar da ci gaban cinikin waje. A shirye take wajen tunkarar duk wata barazana daga waje cikin dogon lokaci. Kana tana da aniya da kwarewa wajen ci gaba da jawo jarin waje, tare da samar wa duniya damar ci gaba. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China