Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta gina rumbun musayar bayanai na shiyya
2020-07-17 13:13:20        cri
A ranar Laraba ne, lardin Hunan dake yankin tsakiyar kasar Sin, ya fara gina wani katafaren rumbun musayar bayanai na shiyya, a wani sabon mataki na cin harkokin tattalin arziki na zamani dake bunkasa a halin yanzu.

Tsarin musayar, zai mayar da hankali ne kan cinikayyar bayanai dake da nasaba da harkoki na sadarwa, da zirga-zirga, da taswira, baya ga sauran bayanai na harkokin kudi da su ma za a rika cinikayyarsu bisa doka.

A cikin watan Disamba ne dai, ake fatan kammala gina cibiyar musayar, wadda aka gina ta da jarin Yuan miliyan 300, kwatankwacin dala miliyan 42.9.

Sai dai a sakamakon matsin lamba da tattalin arziki ke fuskanta, ya sa kasar Sin take neman Karin jari a sabon tsari na more rayuwa, kamar tsarin fasahar 5G, da manyan cibiyoyin adana bayanai da sauran ayyuka dake taimaka ga kirkire-kirkire, da karfafa sassa masu rauni a fannin tattalin arziki da jin dadin jama'a. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China