Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ci gaba tattalin arizkin Sin na taimakawa kasa da kasa wajen farfado da tattalin arzikinsu
2020-07-17 13:54:59        cri

Hukumar kididdiga ta kasar Sin (NBS) ta sanar a ranar 16 ga wata cewa, alkaluman GDPn kasar ya karu a rubu'i na biyu na shekarar bana, karuwar kaso 3.2 cikin 100 kan makamancin lokaci na bara. A yayin da muke fuskantar matsalar yaduwar cutar COVID-19, farfadowar tattalin arzikin Sin ya kara imanin kasa da kasa wajen farfado da tattalin arzikinsu.

Shugaban cibiyar nazarin tattalin arzikin kasa da kasa ta Peterson ta kasar Amurka Adam Posen ya bayyana cewa, managartan matakai da kasar Sin ta dauka cikin gaggawa domin dakile yaduwar cutar COVID-19, sun taimaka wajen farfado da tattalin arzikinta fiye da na sauran kasashen duniya. Kana, jaridar Financial Times ta kasar Burtaniya ta wallafa wani bayani cewa, jerin matakan da kasar Sin ta dauka da suka hada da, samar da karin rancen kudade, taimakawa kamfanoni masu fama da matsaloli, da inganta tsarin samar da kayayyaki da sauransu, sun ba da tabbaci ga farfadowar tattalin arzikin kasar.

Yanzu, duniya na ci gaba da fuskantar sauye-sauye, kasar Sin tana tsayawa tsayin daka wajen bude kofa ga waje, lamarin da ya samar da damammaki ga kasuwanni cikin gida, wanda ya kuma janyo hankulan masu zuba jari na kasa da kasa. Sabo da a ganinsu, zuba jari a kasar Sin ya kasance matakin cimma moriyar juna, kana, nasarar da kasar Sin ta cimma wajen dakile yaduwar cutar ta kara musu Imani kan farfadowar kasuwannin kasar. A rubu'i na biyu na shekarar bana, takardun bashi da masu zuba jarin kasashen ketare suka saya daga kasar Sin ya karu da kaso 48 cikin dari kan makamancin lokaci na bara.

Karuwar alkaluman GDPn kasar Sin a rubu'i na biyu ya sa kaimi ga kasa da kasa, ko da yake, akwai jan aiki a gabanmu wajen farfado da tattalin arziki baki daya, sabo da matsalolin da yaduwar annobar cutar COVID-19 ta haifar mana, wadanda ba a taba ganin irinsu ba, amma, kasar Sin za ta iya fuskantar dukkanin kalubalolin dake gabanta, bisa ingancin tattalin arzikin ta, da kuma wasu matakan da take da su ta fuskar kare ci gaban tattalin arzikinta, kamar, kara bude kofa ga waje, da manufofin tallafawa bangarorin da abin ya shafa da sauransu, ta yadda, za ta iya ba da gudummawa ga kasa da kasa wajen farfadowar tattalin arziki bai daya. (Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China