Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin na son hada kai da kasashen duniya wajen yaki da annobar COVID-19 da daidaita sauran kalubaloli
2020-07-20 21:17:55        cri

Wang Wenbin, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana yau Litinin a nan Beijing cewa, kasar Sin na son hada kai da kasashen duniya wajen tabbatar da kasancewar sassa daban daban a duniya, da yaki da annobar cutar numfashi ta COVID-19 da daidaita sauran kalubaloli tare, a kokarin raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan 'yan Adam.

Kwanan baya, António Guterres, babban sakataren MDD ya bayyana cikin jawabinsa a yayin taron manyan jami'ai na kwamitin MDD mai kula da tattalin arziki da jin dadin jama'a cewa, yaduwar annobar ta COVID-19 ta nuna muhimmancin inganta da sake yin alkawarin tabbatar da kasancewar sassa daban daban tare cikin hadin gwiwa a duniya. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China