Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban yankin Sin ya gano karin sabbin masu dauke da COVID-19 18
2020-06-22 13:18:51        cri

Hukumar lafiya ta kasar Sin, ta ce ta samu rahoton gano karin mutane 18 dake dauke da cutar numfashi ta COVID-19 a jiya Lahadi a babban yankin kasar, ciki hadda mutane 11 da suka harbu da cutar a cikin gida, da kuma mutane 7 da suka shigo da ita daga ketare.

Alkaluman sun nuna cewa, cikin mutane 18 da suka harbu da cutar a cikin gida, mutane 9 na a birnin Beijing, da kuma mutane 2 a lardin Hebei mai makwaftaka da birnin na Beijing. To sai dai kuma hukumar ta ce, ba a samu rasa rayuka sakamakon sake bullar cutar ba.

Ya zuwa Lahadi, jimillar masu dauke da cutar COVID-19 a babban yankin na Sin sun kai mutum 83,396, ciki hadda mutum 349 da a yanzu ke samun jinya, da kuma mutane 12 dake cikin mawuyacin hali.

Kaza lika ya zuwa wannan rana dai, adadin wadanda cutar ta harba a yankin musamman na Hong Kong ya kai 1,131, ciki hadda mutane 5 da cutar ta hallaka. Har ila yau cutar ta harbi mutane 45 a Macao, da mutane 446 a yankin Taiwan, ciki hadda mutane 7 da suka rasu sakamakon cutar. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China