Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yiwa mutane kimanin miliyan 10 gwajin COVID-19 cikin kwanaki 19 a Wuhan
2020-06-03 10:50:21        cri

Rahotanni daga birnin Wuhan dake lardin Hubei a yankin tsakiyar kasar Sin na cewa, an yi nasarar yiwa mazauna birnin kimanin miliyan 10 gwajin cutar COVID-19 cikin kwanaki 19 na tantance masu dauke da cutar.

Daga ranar 14 ga watan Mayu zuwa 1 ga watan Yuni, an yiwa mazauna birnin 9,899,828 gwajin cutar, kuma ya zuwa jiya Talata, ba a samu rahoton ko da mutum guda da ya kamu da cutar ba. Sai dai an killace mutane 300 da suka kamu da cutar kuma suka warke ba tare da nuna alamu ba. Haka kuma, an killace dukkan mutane 1,174 da aka tabbatar sun yi mu'amula da wadanda aka gwada ba su da alamun cutar.

Shi dai wannan gwaji da ake yi kyauta ne, gwamnati ce za ta biya dukkan kudaden. Yanzu haka birnin na Wuhan ya kashe Yuan miliyan 900, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 126 wajen yin gwaje-gwaje, matakin da ya baiwa mazauna birnin da ma kasar Sin baki daya tabbaci, baya ga taimakawa birnin wajen dawo da harkokin tattalin arziki da zamantakewa kamar yadda suke a baya. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China