Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ofishin jakadancin kasar Sin ya taimakawa yaran kasar Ghana da kayayyakin yaki da annobar COVID-19
2020-04-29 11:02:11        cri

Yayin da ake tsaka da yaki da cutar COVID-19, ofishin jakadancin Sin dake Ghana, ya ba da kayayyakin yaki da annobar ga gwamnatin kasar, domin kula tare da kare yara masu rauni.

Kayayyakin sun hada da kwalaben sinadarin tsaftace hannu 1,200 da kunshin kyalle tsaftacce najasar yara guda 6,800 da marufin baki da hanci 3,000 da sabulu 2,520 da toilet paper 1,200.

Da yake gabatar da kayayyakin, jakadan kasar Sin a Ghana Wang Shiting, ya ce cutar COVID-19 na shafar kowa da kowa, ciki har da yara masu rauni.

Ya ce ofishin jakadancin da hadin gwiwar cibiyar 'yan kasuwar kasar Sin a Ghana ne suka ba da gudunmuwar kayayyakin bukatun domin rage matsi ga gidajen marayu da na raino da kuma taimakawa yara masu rauni a kasar.

Da take karbar kayayyakin, Ministar kula da batun jinsi da yara da walwalar jama'a, Cynthia Morrison, ta godewa ofshin jakadancin da cibiyar 'yan kasuwar kasar Sin dake Ghana, bisa gudunmuwar da suka ba yaran kasar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China