2020-06-22 14:26:36 cri |
Rahotanni daga birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, sun tabbatar da dakatar da ayyuka a daya daga masana'antun kamfanin PepsiCo dake yankin Daxing na birnin, bayan da a ranar Asabar, aka samu rahoton harbuwar ma'aikatan kamfanin su 8 da cutar numfashi ta COVID-19.
Yayin wani taron manema labarai da ya gudana a jiya Lahadi, Pang Xinghuo, mataimakiyar daraktan cibiyar kandagarki da shawo kan cutar na birnin, ta bayyana cewa, biyu daga ma'aikatan da suka harbu da cutar sun je kasuwar kayan lambu ta Xinfadi.
A nata bangaren, jami'a a kamfanin na PepsiCo reshen kasar Sin Fan Zhimin, ta ce masana'antar tasu ta dauki matakan gaggawa, ciki hadda na dakatar da sarrafa kayayyaki, da sauran ayyuka na tattara hajoji, ta kuma yi feshin maganin tsaftace sassan masana'antar, tare da killace ma'aikata.
Bayanai daga shafin yanar gizo na hukumar tattara bayanan kamfanonin kasar, sun nuna cewa, masana'antar da wannan lamari ya shafa, na sarrafa kayayyaki daga hatsi, da tumatur da wasu nau'ikan fanke.
Daga ranar 11 ga watan nan na Yuni kawo yanzu, an samu karin masu dauke da cutar COVID-19 sama da 200 a birnin Beijing, mafi yawansu na da alaka da kasuwar kayan lambu ta Xinfadi. (Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China