Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An sallami wani mutum da ya kamu da COVID-19 daga asibiti a babban yankin kasar Sin
2020-06-03 10:38:01        cri

Hukumar lafiya ta kasar Sin ta sanar a yau Laraba cewa, an sallami wani mutum daga asibiti jiya Talata a babban yankin kasar, bayan da aka tabbatar ya warke daga cutar.

A bayanan rana-rana da hukumar take fitarwa game da yanayin cutar, ta ce har yanzu haka, akwai marasa lafiya 73 dake karba magani a asibitocin kasar

Rahoton hukumar ya nuna cewa, ya zuwa jiya Talata, baki daya, an sallami marasa lafiya 78,314 daga asibitoci daban-daban a kasar, bayan da aka tabbatar sun warke daga cutar. Haka kuma ya zuwa jiyan, an ba da rahoton jimillar mutane 83,021 da aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a babban yankin kasar ta Sin, kana cutar ta halaka mutane 4,634.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China