Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministan kasar Sin ya yi jawabi a taron kolin samar da alluran rigakafi na duniya
2020-06-05 10:59:18        cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bayyana cewa, kasarsa za ta ci gaba da goyon bayan rawar da MDD ke takawa na jagorantar aikin binciken samar da alluran rigakafi, a yayin da take ba da gudummawa don tabbatar da cewa, kasashe masu tasowa sun samu alluran cikin sauki da kuma araha.

Li ya bayyana haka ne, yayin da yake jawabi a taron kolin samar da alluran rigakafi na duniya da aka shirya ta kafar bidiyo, kan yadda kasashen duniya za su tara kudaden samar da ma wadatuwar alluran rigakafi a duniya (GAVI)

A baya ma, Firaminista Li ya bayyana yayin bude babban taron lafiya na duniya(WHA) da ya gudana a watan da ya gabata cewa, kasar Sin tana shirin gina tsarin lafiyar al'ummar duniya da zai shafi kowa da kowa, har ma ta gabatar da wasu shawarwari da matakai, kan yadda duniya za ta hada kai wajen yaki da annobar cutar numfashi ta COVID-19.

Ya kara da cewa, kasarsa za ta ci gaba da taimakawa kasashe yakar annobar COVID-19, gwargwadon karfinta, ta yadda za su farfado da tattalin arziki da zamantakewa, musamman kasashe masu tasowa.

Ya ce, kasar Sin tana gudanar da binciken kimiya game da rigakafin cutar COVID-19, da magunguna da na'urorin gwaje-gwaje. Haka kuma kasar Sin tana dora muhimmanci kan hadin gwiwar kasa da kasa a fannin bincike da samar da alluran rigakafi.

Li ya kara da cewa, akwai kyakkywar alaka tsakanin kasar Sin da gamayyar GAVI, tana kuma goyon bayan kokarin kasar na yin rigakafi da ma yadda za a gudanar da rigakafin a kasashen duniya. Daga karshe, ya bayyana kudirin gwamnatin kasar Sin na taimaka wa gamayyar GAVI da kudaden tafiyarwa, da karfafawa cibiyoyi da kamfanonin bincike da samar da alluran rigakafi na kasar gwiwar karfafa hadin gwiwa da GAVI, da goyon bayan muhimmiyar rawar da GAVIn ke takawa na yayata amfani da alluran rigakafi.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China