Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
G20 ta yi alkawarin daukar dukkan matakai don goyon bayan farfado da tattalin arzikin duniya
2020-07-19 17:37:32        cri

Ranar 18 ga wata, ministocin kudi da shugabannin manyan bankunan kasashe mambobin kungiyar G20 sun shirya wani taro ta kafar bidiyo. Wata sanarwar da aka bayar bayan taron ta bayyana cewa, kungiyar G20 ta yi alkawarin ci gaba da daukar dukkan matakai don tabbatar da kyautata zaman rayuwar al'umma, da samar musu ayyukan yi, da tabbatar da isasshen kudin shigarsu, da goyon bayan farfado da tattalin arzikin duniya, da inganta yadda tsarin hada-hadar kudi yake daidaita barazana yadda ya kamata, da kuma yin rigakafin koma bayan tattalin arziki.

Sanarwar ta sake nanata goyon bayan yadda asusun bada lamuni na duniya wato IMF yake taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da tsaron hada-hadar kudi a duniya. Ta kuma yi maraba da a baiwa aususun tallafin kudi, a kokarin kyautata kwarewar asusun wajen daidaita barazana da kuma warware matsalar karancin kudi da wasu kasashen da suke da karancin kudaden shiga suke fuskanta. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China