Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
G20 za ta zuba dala triliyan 5 ga kasuwar duniya don tinkarar COVID-19
2020-03-27 14:41:19        cri

Kungiyar G20 ta sanar a jiya Alhamis cewa, kungiyar tana daukar matakai masu inganci ciki hadda zuba dala triliyan 5 ga duniya don tinkarar COVID-19.

A jiya ne, aka kira taron shugabannin kungiyar G20 ta kafar bidiyo don tattauna yadda za a magance wannan cutar. A sanarwar bayan taron da aka fitar, shugabannin kasashen da suka halarci taron sun bayyana cewa, G20 za ta yi kokarin fito da daukar matakan da suka dace, don magance illar da cutar ta haddasa ga tattalin arziki da ma al'ummar duniya, da farfado da bunkasuwar tattalin arzikin duniya da ba da tabbaci ga dorewar kasuwannin da kara karfin tattalin arzikin duniya na jure duk wani hadari da zai iya fuskanta. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China