Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta gabatarwa G20 shawarar hadin gwiwa domin tabbatar da daidaito a fannin samar da hajoji ga duniya
2020-03-31 11:23:00        cri

Ministan cinikayya na kasar Sin Zhong Shan, ya ce Sin na fatan kasashe mambobin kungiyar G20 za su yi aiki tare, wajen tabbatar da daidaito a hada-hadar masana'antu, da tsarin samar da hajoji na duniya.

Zhong Shan ya ce akwai bukatar dukkanin sassa su aiwatar da matakan da suka wajaba, na rage ko soke haraji, da kawar da shingen cinikayya, da samar da managarcin yanayin cinikayya tsakanin kasa da kasa.

Ministan ya gabatar da wannan shawara ne a jiya Litinin, yayin taro ta kafar bidiyo da ya gudana, game da tattauna matakan dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, wanda ministocin cinikayya da zuba jari na kasashe mambobin kungiyar G20 suka halarta.

Zhong ya ce yana fatan mambobin G20 za su fadada hadin gwiwar kasa da kasa wajen kandagarkin cutar, da kuma samar da kayayyakin bukata na lafiya, domin karewa, da tsaron lafiyar al'umma, da ma'aikatan lafiya a dukkanin kasashen duniya.

Yayin tattaunawar, daukacin ministocin cinikayya da zuba jari na kasashe mambobin G20, sun sha alwashin ci gaba da samar da muhimman kayayyaki, musamman na kiwon lafiya da magunguna, yayin da ake yaki da wannan annoba a duniya.

Bugu da kari, ministocin sun fitar da takardar bayan taro kan shafin yanar gizo, na babban sakataren G20 na fadar masarautar Saudiyya, suna masu bayyana damuwa game da kalubalen da ma'aikata da 'yan kasuwa ke fuskanta, musamman a yankunan da ake fuskantar wannan annoba.

Sanarwar ta kuma jaddada muhimmancin aiki tare, domin tallafawa kanana da matsakaitan masana'antu, su kuma lura da muhimmancin karfafa hada-hadar zuba jari a matakin kasa da kasa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China