2020-04-20 13:12:48 cri |
A wannan rana, kasar Saudiyya, dake shugabantar kungiyar a wannan karo, ta jagoranci gudanar da taron ministocin lafiyar na kasashe mambobin kungiyar G20 ta kafar bidiyo, jami'an da suka halarci taron sun yi musayar ra'ayoyi kan fasahohin yaki da cutar numfashi ta COVID-19, da kuma matakan da suka dauka domin dakile yaduwar annobar.
A yayin taron, ministocin sun fidda wata sanarwa cewa, dukkanin manufofi da matakan sun fidda su ne domin kiyaye lafiyar al'umma da kuma ba da tallafi gare su, da yaki da cutar, kana da karfafa ayyukan kiwon lafiyar kasa da kasa da kuma rage hasarar da wannan annoba za ta yiwa tattalin arzikin duniya.
Haka kuma, an ce, ministocin lafiyar kasashen G20 za su dauki karin matakai don hana yaduwar cutar COVID-19, kuma za su sake kiran wani taro a nan gaba idan bukatar hakan ta taso. (Maryam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China