Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta gabatar da shawararta a yayin taron G20 don yakar COVID 19
2020-03-27 13:18:30        cri

Jiya Alhamis da dare ne, Shugaba Xi Jinping da sauran shugabannin G20 sun halarci wani taro na musamman da aka kira ta kafar bidiyo. Inda shugabannin suka tattauna kan yadda za a magance cutar COVID 19, ganin yadda take kara yaduwa a duniya. Xi Jinping ya ba da shawarar amfani da fasahar kasar Sin don tallafawa duniya gaba daya.

Daren jiya, shugaba Xi ya yi jawabi mai taken "Hada kai don yaki da COVID-19 ", ana iya fahimtar dabarar Sin cikin muhimman jimloli uku.

Ta Farko: Kara taimakawa juna

Shugaba Xi ya ce, annoba makiyin daukacin Bil Adama ne. A halin yanzu, kamata ya yi kasashen duniya su karfafawa juna gwiwa da kara hadin kai don tinkarar cutar tare.

Ta biyu: Ingata hadin kai

Shugaba Xi ya yi kira a gun taron cewa, hadin kan bangarori daban-daban na duniya don kandagarki da dakile yaduwar cutar tare, shi ne mataki mafi inganci da Sin take dauka wajen cimma nasarar wannan cuta a kasar. Kamata ya yi, kasashe daban-daban sun kara hada kai don kafa wani tsari mai inganci wajen yakar wannan cutar tare.

Ta uku: kara tuntubar juna

Cutar ta illata tattalin arziki da zaman al'ummar duniya matuka, musamman ma a fannoin samar da kayayyaki da biyan bukatun yau da kullum na duniya, lamarin da ya sa tattalin arzikin duniya ke fuskantar koma baya. Don haka, shugaba Xi ya yi kira ga gwamnatocin kasa da kasa da su kara tuntuba a tsakaninsu kan manufofin tattalin arziki, da tsara manufofin kudi masu inganci, ta yadda za a tabbatar da darajar kudi. Ban da wannan kuma ya ce, kamata ya yi a kara sa ido kan batun hada-hadar kudi da kiyaye ingancin kasuwar hada-hadar kudi, da ba da tabbaci ga sha'anin samar da kayayyaki a duniya cikin hadin kai.

Kazalika, shugaba Xi ya bayyana a gun taron cewa, Sin za ta kara samarwa kasuwannin duniya kayayyakin harhada magunguna, da na yau da kullum da kayayyakin kandagarkin cutar da dai sauransu. Bugu da kari, Sin za ta ci gaba da ba da gudunmawarta ga dorewar tattalin arzikin duniya kamar yadda take yi a baya.

Yayin da Shugaba Xi Jinping ya ziyarci kasar Faransa a ran 26 ga watan Maris na shekarar bara, ya taba yin jawabin cewa, "Kamata ya yi kasa da kasa su sauke nauyin dake wuyansu yayin da ake fuskantar kalubale, da kuma daukar matakai masu amfani da inganci a maimako yin biris, a kokarin tabbatar da makomar bil Adama a hannunmu." Har ila yau, wannan furucin na da amfani matuka ga duk duniya gaba daya. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China