Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministocin ciniki da zuba jari na kungiyar G20 sun lashi takobin shawo kan mummunan tasirin COVID-19
2020-05-15 10:55:00        cri

Ministocin ciniki da zuba jari na kasashen kungiyar G20, sun yi alkawarin hada hannu wajen shawo kan tasirin COVID-19 kan harkokin ciniki da zuba jari.

Cikin wata sanarwa da aka fitar bayan taron da suka yi ta kafar bidiyo a jiya, ministocin sun amince da shirin "matakan G20 na tallafawa harkokin ciniki da zuba jari na duniya domin tunkarar COVID-19", wanda kwamitin kwararru mai kula da ciniki da zuba jari na kungiyar ya tsara.

Daga cikin matakan, masu cin gajerin zango, na da nufin saukaka tasirin COVID-19, yayin da na dogon zango za su taimakawa sauye-sauyen da ake bukata a kungiyar cinikayya ta duniya WTO da kuma tsarin ciniki tsakanin kasa da kasa.

Har ila yau, Ministocin sun bayyana jajircewarsu wajen bada gudunmuwa ga shimfida tubali mai kwari ga farfado da tattalin arzikin duniya, bisa ci gaba mai karfi da dorewa da daidaito da zai kunshi dukkan bangarori. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China