Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na fatan tabbatar da nasarorin da aka cimma a gun taron kolin G20 a kokarinta da kasashen duniya
2020-03-27 19:53:35        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya ce an cimma nasarar shirya taron koli na musamman na kungiyar G20, game da tinkarar cutar COVID-19 a ranar 26 ga wata. Kuma kasar Sin na fatan kokari tare da kasashen duniya, don tabbatar da nasarorin da aka cimma a gun taron kolin.

Kakakin ya bayyana haka ne a yau Juma'a a nan birnin Beijing, inda ya kara da cewa, sanarwar da aka zartas, ta nuna alama mai yakini ta kara hadin kai a tsakanin kasashe mambobin kungiyar G20, don tinkarar annobar, da kiyaye yanayin karko na tattalin arzikin duniya.

Jami'in ya ce yana cike da imanin cewa, bisa ga kokarin da ake yi, za a farfado da tsarin zaman rayuwa, da ingantawa, da zurfafa hadin kai tsakanin kasashe daban daban, da inganta dauwamammen ci gaban tattalin arzikin duniya cikin daidaito yadda ya kamata. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China