Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kafofin watsa labaran Sin da Afirka sun hada kai domin bayyana labaran yaki da cutar COVID-19
2020-07-17 10:29:19        cri
Cikin taron karawa juna sani na hadin gwiwar yaki da cutar COVID-19 tsakanin kafofin watsa labaran Sin da Afirka da aka kira ta kafar bidiyo a ranar 16 ga wata, shugabannin kungiyoyin 'yan jaridu da wakilan manyan kafofin watsa labarai na kasar Sin da na kasashen Afirka sun cimma ra'ayi daya cewa, ya kamata a inganta hadin gwiwar Sin da Afirka domin yaki da cutar numfashi ta COVID-19, da bayyana labaran yaki da cutar yadda ya kamata.

Kungiyar 'yan jaridu ta shirin "ziri daya da hanya daya" ce ta kira wannan taro, domin hada kan 'yan jaridun kasashen Sin da Afirka, wajen musayar ra'ayoyi kan fasahohin yaki da annoba, da bude wani sabon shafin hadin gwiwar yaki da cutar a tsakanin kafofin watsa labarai na Sin da Afirka. Kuma, 'yan jaridun kasar Sin da suka halarci taron sun bayyana wasu labarai game da hadin gwiwar Sin da Afirka wajen yaki da cutar COVID-19.

Mahalarta taron sun kuma bayyana cewa, ya kamata kafofin watsa labarai na Sin da Afirka su hada kansu, domin kaucewa yada jita-jita da labaran jabu, da yin kira ga kasashen duniya su kare tsarin hadin gwiwar kasa da kasa, da adawa da daukar ra'ayi na kashin kai da ra'ayin nuna wariyar launin fata. Sun kara da cewa, ya kamata a yada labaran gaskiya, da kare ka'idojin yada labarai yadda ya kamata. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China