Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Manyan jami'an kasashen yankunan Gabas ta Tsakiya da arewacin Afirka sun yi kira da a hada kai domin yakar COVID-19
2020-07-15 21:07:51        cri

A ranar 11 ga wata, an gudanar da dandalin "Hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen dake yankin Gabas ta Tsakiya, game da kandagarkin annobar COCID-19.

Taken dandalin dai shi ne "Kara zurfafa zumuncin gargajiya, da gina makoma mai haske tare". Taron wanda ya gudana ta kafar bidiyo a nan birnin Beijing, ya samu halartar manyan jami'ai, da wakilai masana 19, daga kasashe 8, da masana masu ruwa da tsaki 26, daga cibiyoyin nazarin kimiyya da fasahohi na kasar Sin, inda suka tattauna kan batutuwan dake shafar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen dake yankin Gabas ta tsakiya a bangaren kandagarkin annobar COVID-19.

Gaba dayan mahalartan sun nuna cewa, annobar COVID-19 kalubale ce ga daukacin bil Adama, kuma ya dace kasar Sin da kasashen yankin Gabas ta Tsakiya, su kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu, wajen kafa makoma mai haske tare.

Yayin dandalin, shugaban cibiyar nazarin kimiyyar zamantakewar al'umma ta kasar Sin Xie Fuzhan ya bayyana cewa, barkewar annobar ta sa bil Adama kara fahimtar cewa, kasashen duniya suna dogaro da juna, kuma ya dace su hada kai domin ganin bayan wannan annoba.

A nasa tsokaci, shugaban jami'ar Sharjah ta hadaddiyar Daular Larabawa Hamid namiy ya bayyana cewa, kasar Sin ta nuna fifikonta na tsarin mulkin kasa, yayin da take dakile annobar, yanzu haka kuma, Sin da kasashen Larabawa suna gudanar da hadin gwiwa a bangarorin musanyar fasahohin likitanci, da samar da kayayyakin kiwon lafiya, haka kuma suna taimakawa juna, yayin da suke kokarin dakile annobar.

Shi kuwa tsohon firaministan Masar Essam Sharaf cewa ya yi, wayewar kan kasar Sin da na kasashen Larabawa suna kama da juna, don haka ya kamata sassan biyu, su kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu, domin aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya lami lafiya, tare kuma ingiza hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa,(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China