Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD: Akwai bukatar kara azama wajen shawo kan kalubalen lafiya mai nasaba da COVID-19 a yankunan Latin Amurka
2020-07-10 10:22:51        cri

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya yi kira da a kara zage damtse, wajen aiwatar da matakan shawo kan matsalolin lafiya da cutar COVID-19 ta haifar, a yankunan Latin Amurka da Caribbean.

Antonio Guterres, wanda ya yi wannan kira yayin da yake jawabi ta kafar bidiyo a jiya Alhamis, lokacin kaddamar da tsarin aikin dakile cutar daga wadannan yankuna, ya ce "Ya zama wajibi a dauki dukkanin matakai da za su yiwu, don dakile kara bazuwar wannan cuta, tare da dakushe kaifin matsalolin lafiya da wannan annoba ta haifar a yankunan biyu. Ya ce "A wannan gaba da cutar COVID-19 ke ci gaba da yaduwa a sassan duniya daban daban, Latin Amurka da Caribbean, sun zamo sabon sansani da cutar ke bazuwa cikin sauri".

Da yake tsokaci game da tsarin aikin da aka kaddamar, Mr. Guterres ya lasafta wasu matakai da za a dauka a gajere da dogon zango, don cimma nasarar farfado da yankunan cikin sauri. Ya ce kamata ya yi gwamnatoci su kara azama wajen rage fatara, da kamfar abinci, da rashin isasshen abinci mai gina jiki. A cewar sa, ana iya cimma nasarar hakan ta hanyar samar da tallafin kudaden shiga na gaggawa, da na yaki da yunwa. Daga nan sai ya bayyana bukatar gaggauta samar da tallafi daga sassan kasa da kasa domin agazawa kasashe masu bukata. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China