Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwararru daga WHO sun sauka Sin don gudanar da bincike game da tushen cutar COVID-19
2020-07-13 19:33:23        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta ce wasu kwararru 2 daga hukumar lafiya ta duniya WHO, sun iso nan kasar Sin, don gudanar da bincike game da tushen cutar COVID-19.

Hua Chunying ta bayyana hakan ne a yau Litinin, yayin taron manema labarai na rana rana da aka saba gudanarwa. Ta ce kwararrun za su yi hadin gwiwa da masana kimiyya, da takwarorin su kwararru, da masana ilimin likitanci, wajen warware tambayoyin da suka jibanci aikin da za su gudanar.

Jami'ar ta kara da cewa, mai yiwuwa kwararrun su gudanar da makamanciyar wannan ziyara a wasu kasashe da yankuna a nan gaba. Ta ce hukumar WHO ta amince cewa, aikin gano hakikanin tushen wannan cuta ba na gajeren lokaci ba ne, zai kuma shafi ziyartar kasashe da yankuna daban daban dake sassan duniya.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China