Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ma'aikatar wajen Sin ta mika tallafin kayayyakin yaki da COVID-19 ga kungiyar kasashen musulmi ta OIC
2020-07-15 21:04:19        cri

Hua Chunying, ta ce ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta mika tallafin kayayyakin yaki da cutar numfashi ta COVID-19, ga kungiyar kasashen musulmi ta OIC, tuni kuma aka mika kayayyakin ga sakatariyar OICn ta hannun ofishin jakadancin Sin da na kasar Saudiyya a jiya Talata.

Hua Chunying ta kara da cewa, kafin wannan tallafi na yanzu, cikin watanni 6 na farkon wannan shekara, Sin ta mika wasu kayayakin na daban ga kasashen musulmi 54, ta kuma raba dabarun ta na yaki da wannan cuta ga kasashen.

Kayan da kasashe mambobin OICn suka samu tallafi daga Sin a wancan lokaci, sun hada da marufin baki da hanci miliyan 60, da kayayyakin gwajin kwayoyin cutar miliyan 6, da na'urorin tallafawa numfashi sama da 2000. Sauran sun hada da rigunan kariya daga cutar miliyan 10, da na kare idanu, da safar hannu, da sauran kayayyakin kariya da ake bukata, domin kandagarkin wannan cuta.

Daga nan sai jami'ar ta bayyana aniyar Sin, na ci gaba da karfafa hadin gwiwa da kasashen musulmi da kungiyar OIC, wajen aiki tare don yakar wannan annoba, da ma sauran batutuwa na kare lafiyar al'ummun duniya baki daya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China