2020-07-10 11:14:45 cri |
Shahararriyar mujallar ilimin likitanci ta kasar Birtaniya wato "The Lancet", ta watsa wani bayanin da wasu masanan ilimin aikin likitancin kasar Amurka suka rubuta, a jiya Alhamis, inda ta ce yadda kasar Amurka ta janye jikinta daga hukumar lafiya ta duniya WHO wani mataki ne na karya doka, wanda kuma ya haifar da barazana ga tsaron lafiyar daukacin bil Adama.
Wadannan masana, da suka zo daga jami'ar Georgetown ta kasar Amurka, da cibiyar nazarin ilimi mai alaka da aikin likitanci ta kasar, da dai sauran hukumomi, sun rubuta cewa, da ma kasar Amurka ta shiga cikin hukumar WHO ne, bayan da majalisun kasar suka zartas da wani kuduri na MDD na shekarar 1948, kudurin da ya samu goyon baya daga dukkan gwamnatocin kasar Amurka da suka wuce a baya.
A cewar masanan, yadda kasar Amurka ta janye daga WHO zai haifar da mummunan tasiri ga tsaron kasar Amurka, da aikinta na hulda da sauran kasashe, gami da rawar da take takawa a harkokin kasa da kasa.
Masanan sun kara da cewa, bayan da kasar Amurka ta janye jiki daga WHO, ba za ta iya ci gaba da taka muhimmiyar rawa a fannin manyan gyare-gyaren da za a aiwatar da su a duniya ba, maimakon haka, abin da za ta iya yi shi ne tsayawa a gefe ta yi kallo kawai. Sa'an nan kasancewar ta wadda ta yanke hulda da bangarori daban daban, ba za ta iya maye gurbin hukumomin kasa da kasa ba har abada. A duniyarmu dake da bangarori daban daban, rashin bukatar bin wasu ka'idoji, na nufin kasar Amurka za ta rasa damar hadin gwiwa da sauran kasashe. Don tabbatar da tsaron lafiyar jama'ar kasar Amurka, da ta daukacin duniya, ana bukatar yin hadin gwiwa sosai tare da hukumar WHO. Saboda haka, yanke hulda da hukumar zai haifar da babbar matsala ga aikin kare lafiyar jama'a, in ji masanan. (Bello Wang)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China