![]() |
|
2020-07-09 13:41:00 cri |
Haka kuma, ya ce, kasar Sin ba ta son kalubalantar ko yin adawa da kasar Amurka. Dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka tana kawowa tasiri ga kasa da kasa, ya kamata ta samar wa kasa da kasa labarai masu kyau.
Ya kuma kara da cewa, kasar Sin tana son yin hadin gwiwa da kasar Amurka wajen musayar fasahohin yin kandagarki da dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, da habaka hadin gwiwarsu a fannin nazarin allurar rigakafi, da farfado da tattalin arziki. Kuma, ya kamata kasar Amurka ta tsayar da siyasantar da batun annoba, da kuma yin hadin gwiwa da Sin wajen inganta hadin gwiwar kasa da kasa wajen yaki da annobar, domin ceton rayuka, da daukar nauyi a matsayin manyan kasashen duniya yadda ya kamata.
Bugu da kari, Wang Yi ya gabatar da shawarwari guda uku domin kyautata dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, ya ce, ya fi kyau kasashen biyu su sake maido shawarwari dake tsakaninsu, da tsara shirye-shiryen hadin gwiwa da mu'amala, da kuma mai da hankali kan hadin gwiwar yaki da cutar COVID-19. (Maryam)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China